24,99 €
inkl. MwSt.

Versandfertig in 1-2 Wochen
  • Broschiertes Buch

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna yabon Sa muna neman taimakon Sa kuma muna neman gafarar Sa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da sharrin miyagun ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, haka duk wanda Ya batar babu mai shiryar dashi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai bashi da abokin tarayya. Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne. Allah shi yi dadin tsira da albarka ga Manzon Sa Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da duk wanda yabi hanyar…mehr

Produktbeschreibung
Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna yabon Sa muna neman taimakon Sa kuma muna neman gafarar Sa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da sharrin miyagun ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, haka duk wanda Ya batar babu mai shiryar dashi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai bashi da abokin tarayya. Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne. Allah shi yi dadin tsira da albarka ga Manzon Sa Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da duk wanda yabi hanyar su da kyautatawa har ranar tashin kiyama. Bayan haka hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar kuma dukkanin wata bauta a musulunce ba a karbar ta sai anyi ta bisa ilmi kuma bisa koyarwar Manzon Allah (SAW). Manzon Allah yace: "kuzu anni manasika kum" (Ku riki salon aikin hajjin ku daga gareni). "Hajji da Umrah a Saukake" littafi ne dana rubuta shi domin yin bayani game da aikin Hajji da Umrah kamar yadda Manzon Allah ya koyar kuma ya karantar. Na rubuta littafinne da niyyar karantar da alhazai maniyyata aikin hajji, da daliban ilmi da sauran al'ummar musulmi baki daya. Littafin na kasa shi ne bisa babi hudu. Babi na daya zuwa na uku na tattauna ne akan sharudda, rukunai, nau'ukan aikin hajji da yadda ake yin kowane daya daga cikin au'ukan hajjin da abubuwan dake bata hajji. Da kuma muhimman hukunce-hukuncen da suka shafi mata kadai. Sannan babi na hudu kuma na tattauna ne akan ziyara zuwa Madina tare da ladubban ziyarar. Ina rokon Allah madaukakin sarki Ya gafarta wa duk wanda ya karanta wannan littafin, Ya datar dashi sunna da shiriyar manzon Allah (SAW), ya kuma karbe shi gareni a matsayin hidima ga addinin sa. Kuma Allah Ya sakawa wadanda suka taimaka wannan littafi ya tabbata da gidan Aljanna.
Hinweis: Dieser Artikel kann nur an eine deutsche Lieferadresse ausgeliefert werden.